Yadda aka ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas - BBC News Hausa (2025)

Yadda aka ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas - BBC News Hausa (1)

Asalin hoton, Getty Images

Bayani kan maƙala
  • Marubuci, Tom Bateman, Rushdi Abualouf and Lucy Williamson
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News in Washington DC, Istanbul and Jerusalem

Masu tattaunawa tsakanin Isra'ila da na Hamas ba su taɓa hawa ido da ido ba - amma a ƙarshe, hawan bene ɗaya ne ya raba su.

An shafe watanni da dama ana gudanar da tattaunawar tsagaita wuta da masu shiga tsakani daga Qatar da Masar da Amurka, a wasu lokutan ma ba tare da wata kyakkyawan fata ba.

Yanzu duk masu ruwa da tsaki cikin lamarin sun kasance a cikin gini guda a Doha, ana ta kai-komo.

Ana daf da cimma Yarjejeniyar amma a baya al'amura sun sha taɓarɓarewa a mataki makamacin wannan: wata majiya ta bayyana yunƙurin dakatar da wargajewar yarjejeniyar a cikin mintuna na ƙarshe a yayin da ake shirin kafa dandamalin da firaministan Qatar zai sanar da kammalawarta.

"A zahiri, an ci gaba da tattaunawar har minti 10 kafin taron manema labarai. Haka aka samu ɗinke wasu lamura cikin ƙurarren lokaci," in ji majiyar da ke da masaniya kan tattaunawar.

BBC ta tattauna da jami'ai da dama a dukkan ɓangarorin da ke taka rawa a lamarin domin tattaro yadda kwanaki na ƙarshe na shirin da aka gudanar cikin sirri suka kasance.

Sauyin matsaya

Ba kasafai ne aka cimma wannan yarjejniyar ba

Tsarin yarjejeniyar da aka cimma a ranar 15 ga Janairu ya kasance kusan daidai da daftarin yarjejeniyar da Shugaba Joe Biden ya gabatar yayin jawabin da ya yi a Fadar White House a watan Mayun da ya gabata. Ta kuma yi amfani da wannan tsari mai matakai uku da suka haɗa da tsagaita buɗe wuta, da musayar ƴan Isra'ila da aka yi garkuwa da su da fursunonin Falasdinawa da ake tsare da su a Isra'ila, da kuma janyewar sojojin Isra'ila a hankali daga Gaza.

Amma Majiyoyi da ke da alaƙa da tattaunawar sun tabbatar da cewa an sami sauyi kan batutuwan da ake tattaunawa a tsakiyar watan Disamba.

Hamas, wadda a lokacin ke kan farfaɗowa daga jimamain kashe shugabanta Yanhya Sinwar ƴan watannin da suka gabata, ta fara shiga wani halin tsaka-mai-wuya. Ƙawarta ta ƙasar Lebanon Hezbollah ta sha kashi a hannun Isra'ila kuma ta amince da sasanci a tsakaninsu. an kuma fatattaki gwamnatin Bashar al-Assad da ke samun goyon bayan Iran daga Syria.

Ra'ayin Washington shi ne cewa an tilastawa Hamas yin watsi da fatan cewa za a kawo mata ɗauki daga wani ɓangare, in ji wani jami'in gwamnatin Amurka.

Wani babban jami'in gwamnatin Biden da ke da masaniya kan tattaunawar ya ce "Abu ne mai wahala a fayyace yadda al'amura suka sauya da kuma abin da hakan ya yi ga lissafin Hamas."

Yadda aka ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas - BBC News Hausa (2)

Asalin hoton, Reuters

Wani jami'in Isra'ila da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce Hamas ba ta yi gaggawar cimma yarjejeniya ba, kuma ta yi ta ''bayar da umarni ne'' maimakon tattaunawa. Sun ce lamarin ya sauya ne bayan mutuwar Sinwar da kuma farmakin da Isra'ila ta kai kan ƙawayen Hamas a yankin.

Bugu da ƙari, jami'in ya ce, akwai "ƙarin matsin lamba daga gwamnatocin Amurka biyu" - gwamnatin Biden da kuma tawagar Trump da ke hanyar shigowa.

'' Cimma yarjejeniya irin wannan ba zai yiwu ba da al'amura ba su sauya ba.''

A ranar 12 ga Disamba, tawagar gwamnatin Biden ta ziyarci Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na fadar White House Jake Sullivan, da wakilin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya Brett McGurk da daraktan hukumar CIA Bill Burns duk sun halarci taron.

Wani jami'in Amurka, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce taron ya ɗauki tsawon sa'o'i da dama, kuma ya mai da hankali kan "sabon yanayin yankin" da kuma "yadda za mu iya ɗorawa daga yarjejeniyar tsagaita wuta ta Lebanon zuwa wani zagayen tattaunawa mai zurfi" kan Gaza.

  • Tambayoyin da har yanzu ba a san amsarsu ba game da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
  • Abin da muka sani kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
  • Ko tsagaita wuta na iya kawo ƙarshen yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas?

Yadda aka ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas - BBC News Hausa (3)

Asalin hoton, Reuters

Haka kuma a wannan matakin akwai wani ɓangare na tattaunawar da ba za a iya watsi da shi ba: Donald Trump.

A ranar 16 ga Disamba, makonni bayan nasarar Trump, BBC ta yi magana da wani jami'in Hamas da ya bayyana kyakkawar fata game da nasarar yunkurin tsagaita wuta, yana mai nuna cewa an ɗauki lamarin da matuƙar muhimmanci.

Jami'in - wanda ke da hannu a kowace tattaunawa tun daga watan Nuwamban 2023 - ya bayyana cewa mai ba da shawara ga shugaban Amurka mai jiran gado ya aike da saƙo ga masu shiga tsakani da ke nuna cewa Trump na son a cimma yarjejeniya kafin rantsar da shi.

Trump ya kuma yi gargadin "za a ɗauki tsauraran matakai" idan Hamas ba ta amince da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su ba - amma jami'in na falasɗinawa ya nuna turgiya kan annan lamarin.

Jami'in ya ce "A wannan karon, matsin lamba ba zai takaita kan Hamas ba kaɗai, kamar yadda aka saba a ƙarƙashin gwamnatin Biden." "Za kuma a matsawa Netanyahu lamba, shi ne ke kawo cikas ga cimma yarjejeniyar, kuma da alama Trump ya fahimci hakan sosai."

Ta leƙo ta koma

Duk da haka, hasashen da wannan jami'in ya yi cewa za a iya cimma yarjejeniya kafin lokacin Kirsimeti ya ya kasance hadarin kaka ne kawai.

A cikin watan Disamba, tattaunawar ta ci gaba da fuskantar matsaloli. Isra'ila ta fito fili ta yi watsi da sakin wasu manyan fursunonin, yayin da fadar White House ta zargi Hamas da kawo cikas kan batun sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

Wani jami'in gwamnatin Biden ya ce: "Hamas ta ƙi amincewa - kuma hakan ya janyo komai ya tsaya cak a wancan lokacin - ga kuma batun jerin sunayen waɗanda aka yi garkuwa da su da za a saki a matakin farko na yarjejeniyar.

''Wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci. Wannan batu ne na sakin waɗanda aka yi garkuwa da su. Idan har ba ku amince da jerin sunayen waɗanda za a sako ba, babu wata yarjejeniyar da za a cimma.''

Jmi'in ya kuma ƙara da cewa Hamas ta yi iƙirarin da ''ba gaskiya ba''na cewa ba ta san inda aka ajiye waɗanda aka yi garkuwa da su ba. Ya ce ''Mun dage a kai, kuma har mu ka dakatar da tattaunawar har sai Hamasa ta amince da jerin sunayen,''

Yadda aka ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas - BBC News Hausa (4)

Asalin hoton, EPA

Wani jami'in Isra'ila da ba a bayyana sunansa ba ya ce Hamas ta nemi ta ɓoye adadin mutanen da aka yi garkuwa da su waɗanda ke raye kuma "ta yi ƙoƙarin cewa gawarwaki kawai za su sako mana".

A na ta ɓangaren, Hamas ta yi iƙirarin cewa ba zato ba tsammani Isra'ila ta ƙara sunayen mutane 11 cikin jerin mutanen da ta ke son a sako su a matakin farko. Hamas ta ɗauke su a matsayin sojojin ko-ta-kwana, don haka ba za su cancanci a sake su tare da mata, da waɗanda suka jikkata. da kuma tsofoffin da za a sako a matakin farko ba.

An dai bar wata kafa a buɗe ga masu shiga tsakani na Qatar da Masar don ci gaba da yunƙurin da suke yi na shawo kan matsalar, kuma a ranar 3 ga watan Janairu, an sami ci gaba a lokacin da Hamas ta nuƙaci a sako ma ta fursunonin Falasdinawa 110 da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai da rai.

A wannan matakin an riga an tabbatar da sharuɗɗan irin waɗannan musayar. Ga kowane mutum da Hamas za ta saki, Isra'ila za ta ba da wani adadi da aka amince da shi na fursunonin Falasɗinu.

Wani jami'in Amurka ya ce: "Akwai daidaito kan adadin fursunonin Falasdinawan da za su fito. Don haka ga sojoji mata, alal misali, akwai wani adadai na musamman. Kuma ga maza tsofaffi, akwai adadin fursunonin da za a sako. Kuma ga fararen hula mata, akwai na su adadin. Kuma an riiga an amince da wannan tsarin. kuma an bayyana sunayen fursunonin, akwai ɗaruruwan fursunoni a cikin jerin sunayen."

A takardun musayar da aka amince a tattaunawar - fursunonin Falasɗinawa da zako a madadin waɗanda Hamas ta sace - an yi musu laƙabi da "mabuɗai". (''keys'')

Yadda aka ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas - BBC News Hausa (5)

Asalin hoton, Reuters

A cikin wannan mataki na tattaunawar, Hamas ta kuma sassauta kan buƙatu biyu da ta daɗe ta na dagewa a kai: janyewar sojojin Isra'ila gaba ɗaya daga Gaza a matakin farko da kuma Isra'ila ta amince da ƙudurin tsagaita wuta na dindindin.

Da aka fara jin kamshin cimma nasara, mai shiga tsakani na Masar ya aika da Manjo Janar Ahmed Abdel Khaleq cikin gaggawa - wanda shi ne ke kula da bayanan Falasdinawa a a hukumar leken asiri ta Masar - zuwa Doha. Bayan ganawa da wakilan Hamas, ya tabbatar da cewa ƙungiyar kuduri aniyar yanke shawarwarin da wani babban jami'in Hamas ya bayyana a matsayin "masu raɗaɗi."

Amma a ranar 6 ga watan Janairu, a cewar wani jami'in Falasdinu, Isra'ila ta yi watsi da tayin da Hamas ta gabatar kan mutanen 11 da aka yi garkuwa da su. Hamas ta mayar da martani ta hanyar aikewa BBC da wasu kafafen yaɗa labarai jerin sunayen ƴan Isra'ila 34 da aka yi garkuwa da su. Bayan kwana biyu, an ga gawar ɗaya daga cikin waɗanda ke cikin wannan jerin - YosefAlZayadni - a cikin Gaza.

Jerin sunayen ya haɗa da sojojin ko-ta-kwana, wanda ke nuni da cewa Hamas a shirye take ta sake su a matakin farko.

Wannan dai da alama wani yunƙuri ne na kunyata Netanyahu da haɗa kan iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a Isra'ila da ma duniya baki ɗaya domin matsa masa lamba kan amincewa da yarjejeniyar.

Hakan kuma alama ce da ke nuna cewa Hamas ba ta yi watsi da tattaunawar ba.

Tazarar ƴan mitoci kaɗan

A ranakun ƙarshe na tattaunawar, an saba ganin ana kaiwa har yammaci anan gudanar da taruka a birnin Doha.

A cikin watan da ya gabata, sun haɓaka zuwa abin da ake kira "tattaunawar kusanci", inda ɓangarorin biyu ke kasancewa cikin gini guda, a cewar jami'ai da dama da ke da masaniya kan tattaunawar.

Wani babban jami'in Amurka ya ce tawagar Hamas na kan hawa na farko, na Isra'ila kuma a suna hawan da ke saman su. Masu shiga tsakani kuma na ta kai-kom da takarda a tsakanin su. An yi ta sama da ƙasa da taswirorin janyewar sojojin Isra'ila da cikakkun bayanai game da waɗanda aka yi garkuwa da su da kuma fursunonin da aka tsara sakin su.

"Wannan yana ɗaukar aiki mai yawa kuma, gaskiya, ba a cimma matsaya kan batutuwa da dama ba, har sai sa'o'i na ƙarshe," in ji jami'in.

A cikin ginin, tawagogin sun yi ganawa daban-daban da manyan jami'an Qatar da Masar. Daga cikin waɗanda ke da hannu a cikin tattaunawar har da Firaministan Qatar Mohammed bin Abdulrahman Al Thani.

Yadda aka ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas - BBC News Hausa (6)

Asalin hoton, Reuters/Israeli Government Press Office

An dai yi aiki kan wasu muhimman abubuwa guda biyu a matakin ƙarshe na tattaunawar: jerin sunayen mutanen da ƙungiyar Hamas ta yi garkuwa da su da kuma fursunonin Falasdinu da Isra'ila ke riƙe da su, da kuma matsayin janyewar da sojojin Isra'ila za su yi daga yankunan da ke da yawan jama'a a Gaza a cikin matakin farko.

Zuwa ranar 9 ga Janairu, matsin lamba ya ƙaru. Wakilin Trump, da na Biden, da kuma babban jami'in leƙen asirin Masar sun yi taro a Doha, domin wani muhimmin zaman tattaunawa na sa'o'i takwas.

Wani babban jami'in Masar ya shaida wa BBC cewa: "Muna kan matakin kusa da cimma yarjejeniya."

An dai cimma matsaya kan kashi 90 cikin 100 na batutuwan da ba suka rage, amma ana buƙatar ci gaba da tattaunawa.

An tura Steve Witkoff, wanda Trump ya naɗa a matsayin jakadan gabas ta tsakiya kwanan nan zuwa Tel Aviv don ganawa da Netanyahu. Ko da yake har yanzu ba a tabbatar da muƙaminsa a hukumance ba, attajirin nan na New York ya ƙara shiga cikin tattaunawar, wanda Trump ke matuƙar sha'awarsa a kai.

Ana daf da tura shi wani aiki da ya kasance mai mutuƙar muhimmanci.

Ƙarshen batun

Lokacin da mutumin Trump a Gabas ta Tsakiya ya isa Isra'ila a ranar 11 ga Janairu, ranar idabar yahudawa ce.

An buƙaci Witkoff da ya jira har sai rana ta faɗi kafin ya gana da Netanyahu, amma wakilin ya ƙi amincewa da hakan ya kuma buƙaci ya gana da firaministan nan take.

Da alama Netanyahu ya fuskanci matstin lamba a yayin ganawar kuma shiga tsakani daga tawagar Trump don ganin gwamnatin Isra'ila ta jingine shakkun da ta ke da ita game da yarjejniyar ta taka muhimmiyar rawa.

An ba da rahoton cewa ganawar ta kasance cikin kakkausar murya kuma sakon da aka aika wa Netanyahu daga shugaban mai jiran gado ya fito ƙarara: Trump yana son a cimma yarjejeniya - yanzu.

Da yake tsokaci kan wannan tattaunawar, wani jami'in Isra'ila da ya nemi a sakaya sunansa ya ce taron ya yi "matuƙar muhimmanci".

Yadda aka ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas - BBC News Hausa (7)

Asalin hoton, Reuters

Lokacin da Witkoff ya koma Doha, ya ci gaba da kasancewa a cikin ɗakin da ake tattaunawar, inda ya shafe lokaci tare da wakilin Biden Mr McGurk, a wani abin da jami'an Amurka biyu suka kira shirin mika mulki da ba a taba gani ba a fagen diflomasiyyar Amurka.

A wannan makon, jami'in Hamas Bassem Naim ya shaida wa Al Arabiya cewa "ban yi tunanin cewa [yarjejeniyar] za ta yiwu ba, ba tare da matsin lamba daga gwamnati mai jiran gado ƙarƙashin jagorancin Shugaba Trump ba" - kuma musamman ya ba da misali da kasancewar Witkoff a tattaunawar.

Ya zuwa yanzu, batun cewa an kusa cimma yarjejeniyar ya fito fili kuma jama'a sun fara sa rai kan yiwuwar hakan - musamman ma iyalan waɗanda ak yi garkuwa da su da kuma Falasdinawan da suka rasa matsugunansu a cikin Gaza.

A Sa'o'i 72 na ƙarshe na tattaunawar an ci gaba da kai-komo kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar, a cewar wata majiya.

Wata majiyar da ke da masaniya kan tattaunawar ta bayyana yadda aka fayyace "tsari da dabaru" na yadda za a sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza da kuma yunƙurin janyewar sojojin Isra'ila.

A ranar 12 ga watan Janairu, wani babban jami'in Falasdinu da ke da masaniya kan tattaunawar ya ce "dukkan jami'ai suna nan a cikin gini guda", ya ƙara da cewa: "Daren yau na da mahimmanci. Muna daf da kammala cimma yarjejeniyar."

Yadda aka ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas - BBC News Hausa (8)

Asalin hoton, Reuters

Wannan taron ya ɗauki tsawon sa'o'i shida - amma, kamar sau da yawa a baya, an ci karo da tazgaro.

A wannan karon rashin jituwar da ta kunno kai ta shafi tsarin mayar da mutanen da suka yi gudun hijira daga kudancin Gaza zuwa arewacin yankin.

Isra'ila ta so ta binciki mutanen da ke dawowa da motocinsu don tabbatar da cewa ba a yi jigilar ƴan bindiga ko kayan soja ba - wanda Hamas ta ƙi mincewa da hakan.

Masu shiga tsakani sun ba da shawarar cewa ƙungiyoyi daga Qatar da Masar su gudanar da binciken. Ɓangarorin biyu sun amince kuma an warware ɗaya daga cikin batutuwa masu sarƙaƙiya na ƙarshe.

A ranar 15 ga watan Janairu jim kaɗan bayan ƙarfe 18:00, wani mai shiga tsakani na Hamas ya aaikawa BBC wani saƙo cewa: "An gama komai."

Ana shirye-shiryen taron manema labarai.

An cimma Yarjejeniyar da a da kamar ba za ta yiwu ba.

Yadda aka ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas - BBC News Hausa (2025)

References

Top Articles
Latest Posts
Recommended Articles
Article information

Author: Jerrold Considine

Last Updated:

Views: 5701

Rating: 4.8 / 5 (78 voted)

Reviews: 93% of readers found this page helpful

Author information

Name: Jerrold Considine

Birthday: 1993-11-03

Address: Suite 447 3463 Marybelle Circles, New Marlin, AL 20765

Phone: +5816749283868

Job: Sales Executive

Hobby: Air sports, Sand art, Electronics, LARPing, Baseball, Book restoration, Puzzles

Introduction: My name is Jerrold Considine, I am a combative, cheerful, encouraging, happy, enthusiastic, funny, kind person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.